Daga Sada Rumah
Zuri’ar Danwaire daga Karamar Hukumar Batsari sun kai ziyarar ta’aziyya ga Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dr.) Abdulmumin Kabir Usman, kan rasuwar marigayi Sarkin Ruma, Hakimin Batsari.
Ziyarar, wadda aka kai yau a Fadar Sarkin Katsina, ta kasance ne domin jajantawa Mai Martaba bisa rasuwar Sarkin Ruma, wanda ya rasu a lokacin da Sarkin ya ke wajen jihar.

A yayin ziyarar, Mai Martaba Sarkin Katsina ya shawarci ’yan Zuri’ar Danwaire da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da kuma karfafa zumunci a tsakaninsu. Haka kuma ya ja hankalinsu da su ci gaba da raya kyawawan dabi’u da halaye nagari a cikin al’umma.
Da yake jawabi a madadin Zuri’ar, Gado-da-Masun Katsina, Hakimin Wagini, Alhaji Dikko Mu’azu, ya bayyana cewa sun zo ne domin mika sakon ta’aziyyarsu ga Mai Martaba bisa rasuwar Sarkin Ruma.
An gudanar da addu’o’i na musamman domin neman rahama ga marigayi da kuma neman karin lafiya da albarka ga Mai Martaba da daukacin al’ummar Jihar Katsina.

Tawagar ta kunshi Shugaban Karamar Hukumar Batsari, Alhaji Manir Mu’azu; Danwairen Katsina, Dr. Sada Salisu Rumah; da magada da ’yan uwa na marigayi Sarkin Ruma, Alhaji Tukur Mu’azu.


