KATSINA, Najeriya — 18 ga Nuwamba, 2025.
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da kaddamar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Malam Yahaya Masussuka na yin wa’azi da koyarwa da ake ganin sun sabawa ka’idojin shari’ar Musulunci tare da barazana ga zaman lafiya tsakanin al’ummar Musulmi a jihar.
A cewar sanarwar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar (SGS) ya fitar, gwamnati ta samu koken jama’a da kuma na mabiyan Malam Yahaya, wadanda suka yi zargin cewa ‘yan Jama’atu Izalatil Bid’a sun zage shi tare da barazanar kai masa hari.
Domin lalubo maslaha, an tura batun zuwa Majalisar Masarautar Katsina a karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman. Sarkin ya gayyaci Malam Yahaya da wasu malaman addini zuwa fadarsa, inda aka tattauna. A karshen zaman, Sarkin ya ja kunnen dukkan masu wa’azi cewa ba a yarda wani ya yi wa’azi cikin salon da zai zubar da mutuncin wasu Musulmi ko ya sa su ji haushi ba.
Sai dai duk da wannan mataki, gwamnati ta ce ta samu rahotannin da ke nuna cewa matsalar ta ci gaba da wanzuwa. Saboda haka, a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari, ya sanya wa hannu tare da amincewar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, gwamnati ta umurci Malam Yahaya da ya bayyana gaban Kwamitin Ulama don kare kansa kan zarge-zargen da ake yi masa.
Kwamitin zai tantance ka’idoji da tsare-tsaren da masu wa’azi za su bi, sannan duk wanda ya karya wadannan ka’idoji gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace a kansa.

Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankula domin gwamnati na gudanar da lamarin “cikin hikima da adalci.”

