Daga Dr. Sada Rumah
Dr. Sada Salisu Rumah, wanda aka fi sani da Danwairen Katsina, ya bayyana cewa tarin al’adun gargajiya da ke Arewacin Najeriya — masu rinjaye sama da kabilu 250 — na da damar da za su iya tallafa wa ci gaban yankin da kuma dore masa, idan aka sarrafa su yadda ya kamata.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da takardar sa a wajen rufe bikin Arewa Fashion and Food Festival (AFFEST) 2025, da aka gudanar a Lumana Centre, Kaduna.
A cikin takardar da ta ɗauki taken “Irin Gudummawar da Al’adu Za Su Iya Bayarwa Wajen Haɗa Kan Arewacin Najeriya,” Dr. Rumah ya ce yankin Arewa na da albarka ta al’adu iri-iri da kuma yawan jama’a da ya haura miliyan 150.
Ya bayyana cewa duk da bambancin kabilu da harsuna, Arewacin Najeriya na da ɗaurewar zumunci da dabi’u na bai ɗaya da suka samo asali daga al’adun gargajiya, abin da ya taimaka wajen karfafa haɗin kai tsakanin al’ummomi daban-daban na addinai da asali.
Dr. Rumah ya ce duk da kalubalen da ke tattare da tasirin al’adun Turawa, ci gaban birane, rashin rubuta tarihin al’adu, da kuma tasirin kafafen sada zumunta da matsin tattalin arziki, al’adun Arewa har yanzu suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar jama’a.
Ya bayyana AFFEST a matsayin “ƙaddararre kuma kishin ƙasa” da matasan Arewa suka kirkira domin haɗa ci gaban zamani da kiyaye al’adun gargajiya. Ya ce idan aka kula da wannan biki yadda ya kamata, zai iya zama hanyar bunƙasa tattalin arziki ta yawon bude ido, ƙarfafa zumunci tsakanin al’umma, da kuma tallata kyakkyawan sunan Arewa a matakin ƙasa da duniya.
A nata jawabin maraba, Babbar Mai Kula da AFFEST, Barrister Bilqees Abdurrashid Shebby, ta ce an kafa wannan biki a shekarar 2023 domin dawo da labarin gaskiya na Arewa da kuma nuna wa duniya kyawun al’adunta, zurfinta da hazakarta.
Ta bayyana cewa, “AFFEST ya fara ne a matsayin motsi na farkar da al’adu, nuna alfahari, da kuma ƙarfafa kai.” Ta ƙara da cewa a bana (2025), an mai da hankali ne kan murnar launuka, sautuka, da kyawawan al’adun al’ummomin Kudancin Kaduna.

Bikin ya bai wa masu sana’o’in hannu da kungiyoyin al’adu dama su nuna fasaharsu da basirarsu ta hanyar nune-nune da gasa.
Barrister Bilqees ta ce babban burin AFFEST shi ne ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummomin Arewa, tare da tabbatar da cewa bikin zai ci gaba da bunƙasa da kuma zaburar da sauran kabilu a duk faɗin yankin.
Ta ce, “Abin da AFFEST ke murnar yi a shekarar 2025 ba kawai biki na al’adu ba ne, amma wani motsi ne na farfadowa da martabar al’adun Arewa.”
Fitattun abubuwan da suka ƙayatar a bikin sun haɗa da raye-raye da waƙoƙi daga kungiyoyi kamar Matan Yabo da Tabs Cultural Troupe, nune-nunen abinci, fasaha da kayan hannu, gasar kayan ado, da tattaunawa kan yadda za a ƙirƙiri ayyukan yi da bunƙasa baiwa a tsakanin matasa.


